1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC: 'Yan takara 144 ke neman shugabancin Najeriya

Uwais Abubakar Idris
January 18, 2019

Hukumar zaben Najeriya ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasar da mataimakansu a zaben da za’a gudanar a wata mai zuwa wanda ya nuna 'yan takara 144 za su fafata a zaben.

https://p.dw.com/p/3Bo9s
Nigeria wählt Gouverneure und Regionalparlamente
Hoto: Reuters/Penney

Jerin sunayen ‘yan takarar neman shugabancin kasa a zaben da za’a gudanar a ranar 16 ga wata mai zuwa a Najeriya ya kasance mafi yawa a tarihin siyasar kasar, abinda a fili ke nuna karuwar masu sha’awar takarar mukaman siyasa.

Akwai dai jiga-jigai a cikinsu da suka hada da jam’iyyar APC da ke mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP wacce wasu jam’iyyu suka kula kawance da ita, sauran kuma kanana jam’iyyu ne da suka hada da matasa. Shin wannan na nuna ci gaba ne ga siyasar Najeriyar?

Nigeria Wahlen 2011 Bild 2
Wasu masu aikin zabe a NajeriyaHoto: DW/Gänsler

Akwai mata 28 da ke cikin jerin ‘yan takarar tun daga masu neman shugaban kasa zuwa mataimaka da ‘yan majalisun tarayya da jihohi. Hajiya Umma Abdullahi ‘yar takarar mataimakin shugaban kasa ce a jamiyyar Young Progressive Party.

Hukumar zaben Najeriya dai ta bayyana cewa a sabon salo a zaben za’a gudanar da tantance masu jefa kuri’a ne ana kuma yin zabe a lokaci guda.

A yayainda ya rage kasa da wata guda a gudanar da zaben na Najeriya, shigar matasa  takarar mukamai a inuwar jamiyyun kasar na nuna samun sauyi sannu a hankali wanda ya zo sakamakon dokar da ta baiwa matasan damar shiga a dama da su a sha’anin shugabanci.