1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garkuwa da daliban jami'a a Najeriya

November 18, 2020

Wasu daga cikin iyayen yara dalibai na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kadunan Najeriya da aka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun roki gwamnatin tarayyar ta taimaka musu.

https://p.dw.com/p/3lVIH
Nigeria Eröffnung Eisenbahnlinie zwischen Abuja und Kaduna
Mutane da dama na bin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja saboda rashin tsaroHoto: DW/U. Musa

Iyayen wadannan yara dai, sun kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da hukumar jami'ar Ahmadu Bello Zariya da su ma su kawo nasu daukin, wajen ganin masu garkuwar sun sako yaran nasu. Masu garkuwar dai, na neman zunzurutun kudin fansa har Naira milliyan 270 kafin su sako daliban har su 12 da aka sace a kan hanyarsu daga Kaduna zuwa Abuja.

Karin Bayani: Gwamnati za ta magance matsalar tsaro

To sai dai an yi dace sakamakon kai daukin gaggawa da wasu jami'an tsaro suka yi, inda kuma suka kubutar da dalibai uku a ranar Lahadin da ta gabata, cikinsu har da wata mace mai jariri da kuma wasu maza biyu da suka sami raunuka. Duk da irin kururuwar da gwanmnati ke yi na cewa ta kubutar da wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su, har ya zuwa wannan lokacin dai akwai sauran dalibai tara da ke a hannun masu garkuwar, mata takwas da kuma namiji guda. Bacewar wadannan dalibai a kan hanyarsu ta Kaduna zuwa Abuja, ya jefa iyayen yara da dangi fadawa cikin rudani da rashin kwanciyar hankali.

Nigeria Katsina Sicherheit
Matsalar tsaro ta sanya matasa yin zanga-zangaHoto: DW/H. Y. Jibiya

Madam Talatu Sani guda ce daga cikin iyayen yara da aka sace, ta kuma yi karin haske: "Tun da safiyar Lahadi Elizabet ta bayyana mana cewa zasu yi wata tafiya da sauran daliban da ke karantar harshen Faransanci daga jami'ar Ahmadu Bello Zaria zuwa Badagri. A lokacin da ita da sauran abokanan tafiyarta suka hadu, ta sake kiran babanta domin gaya masa cewa za su tashi domin kama hanyar tafiya zuwa Abuja. Jim kadan da fara tafiyar aka nemi lambarta aka rasa, tun wannan lokacin ne ake ta yin kokarin ganin cewa an lalubo bakin zaren wannan matsalar domin sanin inda ta shiga."

Karin Bayani: CAN na son a daina zub da jini a Najeriya

Madam Talatu ta ce sun samu yin magan da ita, inda ta shaida musu cewa masu garkuwa da mutane  na bukatar a biya Naira miliyan 30 ga kowane dalibi guda, gaba daya jimillar kudi ta tashi kan Naira miliyan 270 kamin sako dukkanin daliban.  A saboda haka ne take rokon gwamnati da dukkanin masu ruwa da tsaki su taimak wajen ganin an ceto rayuwar daliban. Ta kara da cewa sun tattauna da shugaban sashin tsangayar nazarin harshen Faransanci na jami'ar Ahmadu Bello Zaria, koda yake sun ce suna yin dukkanin kokarinsu wajan ceto su ta dukkanin hanyoyin da suka wajaba.

Karin Bayani: Fafutukar samar da zama lafiya a Kaduna

Mr John Sani shi ne mahaifin wata dalibar da aka sace, dake rokon gwamnatin tarayyar da na jahar kaduna tare da jami'ar Ahmadu bello zaria akan taimakawa ceto 'ya'yansu. Yace sama da shekaru 20 kenan ba shi da aikin yi, kuma shi tsoho ne, bai san inda zai je ya samo wadannan kudi domin ceto rayuwar 'yarsa da aka sace. Kokarin jin ta bakin hukumar makarantar domin sanin irin hobbasar da suke yi dai ya ci tura, sannan ita ma gwamnatin jihar na  nata kokarin. Direbobi da fasinjoji sun fara yin bankwana da bin hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma hanyar Kaduna zuwa Lagos ta Birnin Gwari.