Boko Haram ta tsananta hare-hare a arewacin Najeriya
December 6, 2018Talla
An yi fatan cewa zuwan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi jihar Borno za a samu sauki hare-hare daga Boko haram amma kullum abin karuwa ya ke yi.
Har wayau gwamnatin Najeriya ta bukaci manyan hafsoshin sojojin kasa da da na sama da su koma da zama a shiyyar Arewa maso Gabashn kasar har sai al’amuran tsaro sun inganta lamarin da masana da masharhanta ke ganin ba zai haifar da komai ba tun da ba karo na farko kenan da gwamnatin ke ba da irin wanna umurni ba.