Najeriya: 'Yunwa ta sa 'yan gudun hijirar Borno fusata
February 6, 2019Masu zanga-zanga sun fusata inda suka farfasa wasu kayayyakin gwamnati da kuma allunan talla na ‘yan siyasa, abin da ya haifar da fito na fito tsakaninsu da masu jagaliyar siyasa. Sai dai jami’an tsaro sun shiga tsakani daga bisani. Yawancin ‘yan gudun hijirar sun zabi fitowa kan hanyoyin Maiduguri domin bayyana kokensu na halin da suke ciki na rashin abinci tsawon kwanaki 40, kuma babu alamun za su samu maganin matsalolin.
Wadannan ‘yan gudun hijira sun kuma yi kukan rashin wuraren kwana da sauran kayayyakin rayuwar yau da kullum inda yawanci ke zube a sararin subhana, abin da ya haifar da cututtuka da wasu daga cikin yara da ma tsofaffi saboda sanyi. Da yawa daga cikin ‘yan gudun hijira sun dogara kan barace-barace domin samun abinci, abin da ya sa suke neman taimako daga gwamnati da kungiyoyin jin kai, inda suka ce a maida su garuruwansu ko da mayakan Boko Haram za su kashesu maimaikon su ci gaba da zama 'yunwa ta kashe.
Sai dai hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta musanta wannan zargi da ‘yan gudun hijira suka yi, inda ta ce ba don rashin abinci suka yi wannan zanga-zanga ba, sun yi ne saboda rashin fahimta da aka samu kan rashin gamsuwa da wani rabo da kungiyoyin agaji suka yi a sasanoninsu. A wata sanarwa da kakakin hukumar na kasa Sani Datti ya aike wa manema labarai, hukumar ta ce ta shafe tsawon lokaci na samar da abinci ga ‘yan gudun hijira kuma ba a taba samun tsaiko na rabon kayan abinci a dukkanin sanonin da hukumomi ke kula da su ba.