1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Twitter: Najeriya na shirin dage takunkumi

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 11, 2021

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, za ta dage takunkumin da ta kakabawa kamfanin sadarwa na zamani na Twitter nan ba da jimawa ba.

https://p.dw.com/p/3yrSz
Nigeria | Twittersperre: Mann benutzt Twitter in Lagos
Tun farkon watan Yunin wannan shekarar, Najeriya ta sanya takunkumi kan TwitterHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Cece-kuce tsakanin mahukuntan Najeriyar da kamfanin na Twitter ya samo asali ne, bayan da kamfanin ya goge wani rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar ya wallafa a shafinsa na Twitter, abin da ya sanya gwamnatin dakatar da kamfanin. Dakatar da Twitter din dai, ya janyo koken al'ummomin kasa da kasa dangane da 'yancin fadar albarkacin baki a kasar. A cewar ministan sadarwar Najeriyar Lai Mohammed yana fatan na da 'yan makonni koma kwanaki za a cimma yarjejeniyar da za ta bayar da damar sake bude Twitter din.