SiyasaJamus
Najeriya za ta kaddamar da kudi na Intanet
October 24, 2021Talla
Babban bankin Najeriya CBN, ya ce a ranar Litinin ne zai yi bikin kaddamar kudin kasar na Intanet wato eNaira.
Cikin wata sanarwa, babban bankin Najeriyar ya ce ya shafe shekaru yana gudanar da bincike a kan kudin wanda aka bullo da shi da nufin saukaka wa 'yan Najeriya hanyoyin tafiyar da hada-hada.
A hukumance dai Shugaba Muhammadu Buhari ne zai kaddamar da kudin, kamar yadda babban bankin kasar ya tabbatar.
Bankin na CBN, zai kaddamar da kudin na Intanet ne watanni bayan hana amfani ko hada-hada da irin wannan nau'i na kudi a kasar.
Dama dai an tsara kaddamar da kudin na eNaira ne ranar daya ga watan Oktoba, amma bankin ya dakatar, saboda abin da ya kira cin karo da ranar 'yancin kai.