1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta karbi allurar COVAX

Binta Aliyu Zurmi
February 26, 2021

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce a mako mai zuwa za ta bai wa Najeriya kashin farko na tallafin allurar Covax na rigakafin corona a cigaba da yaki da ake yi da cutar a duniya baki daya.

https://p.dw.com/p/3pzKF
Symbolbild I Erste PFIZER Impfdosen erreichen Kolumbien
Hoto: Guillermo Legaria/Getty Images

A Najeriya, bayan cece-kuce da aka yi tayi kan allurar rigakafin corona, hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da cimma matsaya inda ta ce, an shirya aika allurar kimanin miliyan hudu zuwa kasar mai yawan jama'a a Afirka. 

Wakilin Hukumar ta WHO a Najeriya, Walter Kazadi Mulombo, ya tabbatar da labarin, inda ya ce akalla miliyan goma sha hudu na allurar za kai kasar.

Mulombo ya kara da cewa, akwai bukatar daukar matakin kare jama'a daga annobar duk da cewa cutar bata yadu ainun ba, kamar yadda ake ta yayatawa a lokacin da ta soma bulla.

Ana fatan ganin riga-kafin zai taimaka a kokarin da ake yi na dakile yaduwarta bama a Afrika kadai ba, har ga sauran kasashen duniya da ke fama da masasarar tattalin arziki a sakamakon annobar.