1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasafin kudin gwamnatin Buhari na karshe

October 7, 2022

Gwamnatin Shugaba Buhari na Najeriya ta tsara kashe sama da Naira tiriliyan 20 a 2023—kudin da ba a taba tsara kashe su ba a gwamnatance tun bayan dawowar kasar salon mulkin dimukuradiyya a shekara ta 1999.

https://p.dw.com/p/4Hulz
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Koula Sulaimon/AFP

Kasafin da shugaban ya ce yana da babban burin kai wa ya zuwa kammala manya na ayyukan kasar da gwamnatin ta yinisa a kai dai, ya kunshi naira tiriliyan takwas na kudaden ayyuka na yau da na kullum, a yayin kuma da tiriliyan biyar za su tafi a wajen manya na ayyuka.

Tarrayar Najeriyar dai za ta kashe naira tiriliyan shida wajen biyan kudin ruwa na basukan da shugaban ya ce sun kai naira tiriliyan 42.8

To sai dai kuma abin da ke dauka na hankali cikin kasafin dai na zaman batu na tallafin man fetur da shugaban ya ce ana bukatar a cire shi.

Shugaban dai bai ambaci yawan kudin da gwamnatin kasar ke shiri ta kashe a badin bisa batun na tallafi da ya dauki lokaci yana jawo rikici a tsakanin sassan kasar dabam-dabam ba.

Bangaren zartaswar gwamnatin Najeriyar ya yi amfani hasashen gangar mai miliyan daya da dubu dari shida da casa'in da kasar za ta rika hakowa a duk rana a badi. Ana kuma sa ran sayar da kowace gangar mai a kan dalar Amirka 70.

'Yan majalisar kasar dai na fatan kammala muhawara da yin gyararrakin da suka kamata kafin karshen 2022, inda daga bisa za su mayar wa Shugaba Buhari domin rattaba hannu ya zama doka. Idan har hakan ta samu, gwamnatin Buhari ta yi nasarar kammala tsara kasafin kudi sau uku ke nan tun kafin shiga sabuwar shekara, lamarin da a baya ke zama jidali.