Amurka za ta mika kudin Diezani ga Najeriya
January 10, 2025Talla
Ministan shari'a na Najeriyar Lateef Fagbemi ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce za a yi amfani da kudin da aka kwace daga tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke wajen samar da hasken wutar lantarki a yankunan karkara karkashin wani shirin na Bankin Duniya.
Ya kara da cewa Najeriyar za ta saka miliyan 50 wajen tallafawa shirin na Bankin duniya, wanda zai taimaka wajen inganta karuwar amfani da makamashin da aka sabunta. Sauran miliyan biyu da dubu 88 na dalar Amurkan kuma, za a yi amfani da su ne wajen tallafawa shirin yaki da ta'addanci a kasashen Afirka.