1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta sayar da kamfanin NNPC

Binta Aliyu Zurmi
September 28, 2020

A Najeiya rahotanni na cewa gwamnatin tarayya na shirin sayar da babban kamfanin mai na kasar wato NNPC ga 'yan kasuwa.

https://p.dw.com/p/3j8Eq
BG Regierungssitze | Abuja
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatar da wani kudiri ga majalisar dattawan kasar da ma ta wakilai domin yin dokar za ta bada damar aiwatar da shirin sayar da kamfanin man ga 'yan kasuwa.

An dade ana kai ruwa rana a kan wannan batu na sake kwaskware yadda ake tafiyar da albarkatun kasar, kawo yanzu dai gwamnatin Najeriyar bata mai da martani ba. Sai dai shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawal ya tabbatar da samun kudirin da gwamnatin ta gabatar wanda ya ce za su duba.

Najeriyar da ke zama kasar da ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka arzikin mai, al'ummarta na cikin halin matsanancin rayuwa inda a baya-bayan nan mahukuntan kasar suka kara farashin man fetur din.