1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta shiga matsala saboda dogaro kan mai

May 15, 2020

Masana harkokin tattalin arzikin duniya, sun ce kasar Najeriya ta shiga wani garari sakamakon faduwar da farashin danyen mai ya yi saboda annobar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3cFqb
Erdölindustrie in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/STR

Masanan na cewa hakan ya sanya kasar da ta fi dukiya a Afirka gamuwa da barazanar da ba ta taba gani ba saboda dogaron da ta yi kacokan a kan albarkatun man.

Koda yake hajar na iya farfadowa zuwa wani matsayi na farashi a kan kowace gangar danyen man a kasuwannin duniya, har yanzu da sauran aiki gaban Najeriyar ganin kusan kashi 90% na kudaden shiganta daga man ta dogara.

Ita ma ministar kudin kasar, Zainab Ahmed, ta fada a makon jiya cewar annobar COVID-19 da kuma faduwar darajar makamashin, sun taba Najeriyar matuka.

Najeriyar dai ta yi kasafin kudinta na bana ne a kan mizanin farashin man dala 57 a kan kowace ganga guda.