1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zubar da jini a zanga-zangar Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 5, 2024

Bayan da jami'an tsaro suka yi amfani da karfin tuwo wajen murkushe masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya, masu zanga-zangar kalilan ne suka fito kan titunan manyan biranen kasar.

https://p.dw.com/p/4j8Ot
Najeriya | Zanga-Zanga | Karfi | 'Yan Sanda | Kisa
'Yan sanda sun yi amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP

Rana ta biyar ta jerin gwanon da suka shirya kwashe kwanaki 10 suna yi ke nan, bayan da a ranar Alhamis daya ga wannan wata na Agusta da muke ciki dubban masu zanga-zanga suka bazu a kan titunan manyan biranen kasar da suka hada da Abuja fadar gwamnati da kuma Legos cibiyar kasuwancin Najeriyar da nufin nuna damuwarsu kan tsadar rayuwa da kuma rashin tsaro da ake fama da shi. Sai dai kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa da Kasa Amnesty International, ta ruwaito cewa kimanin mutane 13 ne aka halaka yayin wata arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an 'yan sanda. Amfani da harsasai masu rai wajen hana zanga-zangar da kuma kiran da shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya yi na a dakatar da ita, sun taimaka wajen dusashe kuzarin matasan da suka fito domin neman sauyi a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.