Buhari: Najeriya ta samu ci gaba a cikin shekaru 20
June 12, 2019Talla
Bikin na ranar dimukaradiyya ya gudana a gaban shugabanni na kasashe sama da 20 wanda suka halarci bikin, tuni dai gwamnatin kasar ta sanar da babban filin wasa na kasa da ke a Abuja a matsayin filin kwallon MKO Abiola. Ranar ta zo ga shi kansa shugaban kasar da ke jawabinsa na farko ga 'yan kasar bayan sake dare mulki zuwa mataki na gaba. Cikin wani dogon jawabin da ya dauki sama da mintuna 30 dai shugaban ya ce gwamnatinsa za ta dora a biasa ci gaban da ta samu shekaru Hudu baya. Wannan biki dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun hare-hare a Najeriya na kungiyar Boko Haram wanda Buhari ya ce gwamnatinsa na faman kawo karshen 'yan ta'addar.