Nasarar Tinubu ta mamaye jaridun Jamus
March 10, 2023Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta bayyana Bola Ahmed Tinubu da mazari da ba a san gabanka ba. Ta ce ga mutumin da ba da jimawa ba zai zama shugaban 'yan Najeriya miliyan 220, wanda kuma zai dauki gagarumin nauyi mawuyaci a duniya, akwai tarihi muhimmai guda biyu da ke biye da shi. Na farko shi ne gogaggen dan kasuwa ne da ya shiga siyasa a matsayin hadimin dimukuradiyya, sannan ya rikide ya zama dan siyasa mai aiki da cikawa wanda a matsayin gwamna ya jagoranci birni mafi cunkoso da hargitsi a duniya. Sannan na biyu shi ne mutumin da ya rikirkita tarihinsa da kansa wanda ya yi kudi ta hanyar dillancin kwaya kana daga baya ya zama dan siyasar da ya yi kaurin suna wajen cin hanci cikin rukunin 'yan siyasar Najeriya da suka fi kowa lale kati.
Jaridar ta ce ana yi wa Bola Tinubu kirari da Baba uban kowa, sai dai abin da ba a sani ba shi ne ko wannan yana nufin uba ta fuskar alhairi, tausayi da yakana ko kuwa ya hada dukkan abubuwan? A ranar laraba hukumar zaben Najeriya ta sanar da sunan Tinubu a matsayin wanda ya lashe takarar shugaban kasa mafi zafi da aka fafata a Najeriya tun bayan da kasar ta koma kan tafarkin dimukuradiyya a 1999. Tinubu ya sami kashi 36.6% na kuri'un da aka kada, wadanda suka biye masa na kurkusa su ne Atiku Abubakar da Peter Obi wadanda suka sami kashi 29.1 da kuma kashi 25.4% na kuri'un. Sai dai kokawar ba ta kare ba. 'Yan takarar biyu sun lashi takobin kalubalantar sakamakon zaben.
Jaridar ta Neue Zürcher Zeitung ta ce Tinubu ya yi nasarar lashe zabe da shekarun dattako na shekaru 70. Sai dai shekarun nasa na cike da tababa kamar tarihin rayuwarsa. Mutane da dama suna ganin ya kai shekaru tamanin, suna togaciya da rashin karfin jikinsa da kuma takardun haihuwarsa da suka nuna ranaku mabanbanta. Zababben shugaban na Najeriya Bola Tinubu mai shekaru 70 akwai yiwuwar zai ci-gaba da salon mulki na tsofaffi, tsoho ya gaji tsoho. Matsakaicin shekarun matasa a Afirka dai shi ne shekara 18.
Sabon salon dangantakar Faransa a Afirka
Halascin rashin yarda da manyan kalamai. Wannan shi ne taken sharhin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta kan dangantakar Faransa da Afirka. Emmanuel Macron ya zama tamkar bakon dindindin a Afrika.Shugaban na Faransa ya kai ziyara nahiyar ta Afirka sau goma sha takwas tun bayan da ya hau karagar mulki a 2017. A yan kwanakin nan ya yi ta zabari a ziyarar da ta kai shi kasashen Gabon da Angola da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da kuma Kwango Brazaville. Wannan ba ziyara ce da aka saba ba, sai dai domin shata sabon babin dangantaka, akalla wannan shi ne abin da Macron yake so duniya ta fahimta. Jim kadan bayan da ya sauka Libreville babban birnin kasar Gabon ya yi amfani da manyan kalmomi yana cewa zamanin "Francafrique" ya wuce ma'ana Faransa ba za ta rika tsoma baki a lamuran cikin gida na kasashen Afrika ba.
Macron ya jaddada aniyar kawance da hadin kai da amintaka yana mai cewa Faransa za ta zama mai sauraro ba mai yin danniya ba. Tana so ta taimaka wa ci gaban dimukuradiyya da kasuwanci, amma ba tilasta dabi'un kasarta ba. Shugaban na Faransa ya yi alkawarin dawo da kayayyakin tarihi da aka sace a zamanin mulkin mallaka da kuma rage yawan sojojin Faransa a Afirka.
Jaridar ta ce ko shakka babu sauyi a dangantakar Faransa da Afirka abu ne da ya dace wanda kuma ake bukatarsa. Dangantaka ba ta taba lalacewa tsakanin Faransa da kasashen Afirka ba kamar yadda ta kasance a yau ba. Gwamnatocin Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun fito karara suna adawa da Faransa. Haka ma Burkina Faso ta juya wa Faransa baya. Sai dai duk da haka akwai bukatar yin taka tsantsan a sabon babin da ake son shatawa. Rashin kwakkwarar manufa ta sanya ayar tambaya a kan ko shin da gaske Faransa take a game da sabon babi da Afirka?