Na'urar busar da kayan miya a Najeriya
August 10, 2017Ita dai wannan na'ura da matashin ya kirkiro kan taimaka wajen busar da kayan gwari da nufin adana su don gudun kada su lalace. Kazalika na'urar wacce ta ke amfani da hasken rana yanzu haka an fara amfani da ita a tsakanin masu amfani da kayan gwari a Najeriya. Kusan dai kimanin shekaru sama da uku kenan da suka gabata matashin mai suna Isyaku Mamman ya yunkuro domin kawo wani babban sauyi ga yadda masu safarar kayayyakin gwari daga wannan gari zuwa wancan.
A hirarsa da DW, matashin ya ce kamfar wutar lantarki wadda za a yi amfani da ita wajen adana kayan a furunji ne ya sanya shi tunanin samar da wannan na'ura idan ya kara da cewar baya ga kayan miya, wannan na'ura da ya kirkira kan iya taimakawa wajen busar da duk wani danye kaya da ka iya lalacewa idan ba alkinta shi ba.
Matashin ba wai kawai ya tsaya ga nan ba har ma matasa ya ke nunawa irin yadda za su tsaya da kafafun su. A share guda kuma ya gayawa DW cewar burinsa shi ne ya wayi gari masu safarrar kayan gwari su dinga alkinta kayayyankin su kamar yadda ya dace domin kara bunkasa yanayin harkokin kayan gwari a Najeriya.