1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nazarin sabon albashin jami'an gwamnatin Kenya

Suleiman Babayo AH
July 3, 2024

Fadar gwamnatin Kenya ta ba da umurnin sake nazarin karin albashi ga masu rike da manyan mukaman gwamnati, domin dakile martani daga mutanen da suke ci gaba da fusata kan yadda manyan jami'ai ke wawushe duniyar kasa.

https://p.dw.com/p/4hq0o
Amfani da karfi kan masu zanga-zanga a Kenya
Amfani da karfi kan masu zanga-zanga a KenyaHoto: Shisia Wasilwa/DW

A wannan Laraba fadar shugaban kasar Kenya ta ba da umurnin sake nazari kan karin albashin da aka yi wa masu rike da mukaman gwamnati, a wani matakin na rage zaman tankiya a kasar sakamakon zanga-zangar da aka fuskanta ta nuna kiyayya ga gwamnati, saboda yunkurin kara haraji na kayan da mutane suke amfani da su na yau da gobe.

Karin Bayani: Shugaban Kenya mayar da dokar haraji ga majalisa

Matasan kasar ta Kenya sun fadada bukatar neman ganin Shugaba William Ruto ya ajiye aiki saboda yadda gwamnatinsa ta gaza magance matsalar cin hanci da rashawa gami da bushasha da dukiyar kasa. Gwamnatin Kenya tana shan suka daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam bisa amfani da karfi kan masu zanga-zanga inda kimanin mutane 30 suka halaka lokacin zanga-zangar sannan an kama wasu kimanin 270.