1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nazarin dangantakar EU da kasar Nijar

September 25, 2023

Shugaban kwamitin tsaro da kula da kawancen EU da jamhuriyar Nijar a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, ya shawarci Jamus ta sake yin nazari kan alakar EU da Nijar ba tare da Faransa ba.

https://p.dw.com/p/4WnMl
Majalisar Dokokin Jamus
Majalisar Dokokin JamusHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Dan majalisar na jam'iyyar Social Democratic SPD Christoph Schmidt, ya shaida wa DW cewa akwai bukatar Majalisar Dinkin Duniya  ta san huruminta a yankin Sahel da kuma yin tunani mai zurfi kafin daukar matakin sake kulla alaka da Nijar  ba tare da kasar Faransa ba.


Schmidt ya ce abin da ya kamata a sanya a gaba  shi ne ci gaba da tattaunawa da sojojin da ke mulkin kasar, kamar yadda kasar Amurka ta kudiri aniyar yi, duk da cewa Macron na da hujja cewa har yanzu Bazoum ne halastaccen shugaban kasar don bai yi murabus ba.