'Yan adawa a Jamhuriyar Nijar sun nemi gyara
June 21, 2022A Jamhuriyar Nijar 'yan majalisar na jam'iyyar adawa ta Lumana Afrika wadda madugun yan adawa ya fito daga ciki, sun yi kira ga bangaran masu rinjaye da su bar tsarin tafiyar dimukuradiyya ya gudana yadda ta kamata muddin dai kasa ake son yi wa aiki ba wai son kai ba. Wannan tsokacin ya fito ne bayan wani zama da majalisa ta yi na gyaran fuska ga dokar da ke bai wa madugun 'yan adawan damar gudanar da ayyukansa yadda ta kamata.
Tun dai wajejen shekara ta 2016 ne dai yanayin siyasa da matsayin yan adawa a Jamhuriyar ta Nijar ke fuskantar kon gaba kon baya ta sabili da yadda a cewar yan adawan masu mulki suka hana yan adawar da ma wasu kungiyoyin fararan hulla rawar gaban hantsi bisa dalillai da ke da nasaba da lissafi na siyasa da yadda ta kamata a yi mulki ba tare da cikas ba. Sai dai kuma tuni wasu ke ganin cewa sannu a hankali tun lokaci da Shugaba Mohamed Bazoum ya hau kan karagar mulkin kasar ta Nijar ana samun sauyi da kuma nuna kyaukyawar aniya ta barin lamura su gudana yadda ta kamata a fannin siyasa.
Karin Bayani: 'Yan adawa na Jamhuriyar Nijar sun gana
Sanin kowa ne dai a baya lamarin siyasar kasar ta Nijar ya kai wani matsayi mai cike da muni, inda wasu bangarori na masu mulki da masu adawa suka zabi tozarta juna maimakon bin hanyoyi na dimukuradiyya da nuna da'a ta siyasa ga yan kasa lamarin da a yanzu ya haifar da tabo a zukatan yan siyasa da dama a kasar ta Nijar.
Sai dai a cewar Kane Habibou Kadaure shugaban jam'iyyar SDR Sabuwa da ke bangaran adawa, su dai abin da suka fi son gani shi ne na mutunta dokokin kasa da kiyaye hakkokin 'yan adawa.
A baya dai akwai wannan tsarin na CNDP da ke bada damar walwale duk wani rikici na siyasa, wanda 'yan adawar suka ce masu mulki sun sauya mishi fasali. Sai dai kuma ga masu lura da lamuran siyasar ta Nijar irin su Nassirou Seidou shugaban kungiyar Muryar talaka na ganin cewa shi dai batu da ke hannun shari'a.
Abun jira a gani dai shi ne yadda a nan gaba tafiyar dimukuradiyyar kasar ta Nijar za ta gudana, inda was uke ganin mai yuyuwa shugaban kasa da ke bukatar gudun mowar yan kasa daga kowane bangare, ya kafa wata damba ta tattaunawa ta gaskiya tsakanin yan adawa da masu mulki tare da sallamo fursinonin siyasa irin yadda 'yan adawa ke fada domin dimukuradiyyar ta samu walwala cikin yanayi na nuna son kasar ta Jamhuriyar Nijar fiye da komai.