1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman mafita ga karuwar talauci a Najeriya

July 20, 2023

Gwamnatin Najeriya ta dukufa neman hanyoyin mafita ga barazanar talauci a kasar sakamakon karin farashin mai da daidaita farashin dalar Amurka

https://p.dw.com/p/4UCIP
Standbild Video | Tinubu: 'We anchor well under President-elect Bola Ahmed Tinubu
Hoto: APTN

Wani taron gwamnoni da masu ruwa da tsaki da batun tattalin arzikin tarayyar Najeriya ya kare a Abuja tare da jerin matakai da majalisar ke tunanin na iya kai wa ga kwantar da hankula al'Umma a kasar. Kan gaba a cikin matakan da za a dauka a halin yanzu dai na zaman motoci da samar da abinci da nufin saukaka rayuwar da ke dada kunci. 

A zahiri dai tarayyar Najeriyar tuni ta fara hango haske daga zare tallafin mai tare da matakai na gwamnatin kasar na raba Naira Triliyan biyu ko kuma kaso 300 cikin dari na kudaden da gwamnatocin kasar kan karba. Adadi mafi yawa a tarihin kasar,kuma alamu na kara arzikin 'yan mulki na kasar

To sai dai kuma akwai damuwa bisa makoma ta kasar da a baya kan kalli wasoso da dukiyar al'umma, maimakon hidimar da ke zaman alkawari a tsakanin talakawa da masu mulki. Inuwa Yahaya dai na zaman gwamnan Jihar Gombe, kuma ya ce gwamnonin sun amince su sake tabbatar da amana cikin kasar kan hanyar sake dora kasar bisa turbar dai dai.

Masu mulkin kasar dai na tsakanin gina Najeriya irin ta jari hujja ko kuma komawa zuwa ga tsohon tsari na tallafi tsakanin kowa. To sai dai kuma suna ta faduwar gaba bisa martanin talakawa 'yan rabbana ka wadatanmu da suka kai bango suna ta kumfar baki. Comrade Aminu Abdusallam dai na zaman mataimakin gwamnan Kano da kuma ya ce majalisar ta na karatun gaggawa a cikin neman mafitar matsalar da ke zama mai girma.

Da kyar da gumin goshi ne dai masu mulkin kasar suka kauce wa fushin talakawan kasar shekaru 12 baya, sakamakon kokarin zare tallafin da ya kare da miliyoyin 'yan kasar a tituna.