Neman mafita ga rikicin jam'iyyar PDP a Najeriya
October 15, 2021Masalaha ce ta fitar da farfesa Iyorchia Ayu tsohon shugaban majalisar dattawa kuma tsohon minista na shekaru hudun dake tafe.
Duk da cewar sai ya zuwa karshen watan Oktoban 2021 babban taron jam'iyyar yake shirin tabbatar da shi, bullar Ayun na daukar hankali ciki dama wajen jam'iyyar dake zaman ta biyu mafi tasiri cikin kasar.
Kuma tuni muhawara ta barke a tsakanin 'yan jam'iyyar bisa shugabancin Ayun da kila ma tasirin bisa makomar jam'iyyar dake neman karbar mulki a gaba.
Dr Umar Ardo dai na zaman daya a cikin jiga jigan jam'iyyar daga Adamawa dake fadin bullar Ayun ta saba ka'ida dama dokokin jam'iyyar.
Kokari na kaucewa rikici dai, an kai ruwa rana bisa samar da shugabancin jam'iyyar da kila dan takarar shugaban kasar a zabe na gaba a tsakanin sashen arewacin kasar da kudancinta.
To sai dai kuma nagartar Ayun da ke zaman daya a cikin yaya na kungiyar G18 da ta kai ga haihuwar PDP, ya sa da akwai fatan bude sabon babi ga makomar jam'iyyar a tunanin Comrade Sa'idu Bello dake zaman daya a cikin jiga jigan jam'iyyar a Kano.
Kalubale na farko ga shugaban jam'iyyar dai na zaman iya kai yan lemar zuwa ga fidda gwanin jam'iyyar a zaben shugaban kasar dake tafe.
Rikicin kuma da ya raba kan jam'iyyar a tsakanin arewacin kasar dake kallon share shekaru 16 a mulkin kasar a karkashin tutar jam'iyyar bai isa ba, da kuma dan uwansa dake kudanci na kasar da ke kallon PDP babbar dama ta cika burin komawar mulkin zuwa kudu bayan shekaru takwas a arewa.
Kuma a fadar Faruk BB Faruk dake sharhi a siyasa ta kasar bullar Ayun na tabbatar da rinjaye a bangare na kudanci na kasar dake neman komawar mulki zuwa ga sashe na kudu maso gabashinta.
Gwagwarmayar neman ikon fidda gwanin ne dai ta kai ga majalisar dattawa ta kasar ta amince da wani shirin zaben fidda gwanin na kai tsaye.