1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana neman magance rikicin siyasa a Gambiya

December 13, 2016

Rikicin siyasa a Gambiya bayan Shugaba Yahya Jammeh ya yi watsi da sakamakaon zaben da ya amince da shi tun farko, abin da ya janyo shugabannin kasashen yamma Afirka neman warware rikicin.

https://p.dw.com/p/2UCNT
Gambia Wahlen Yahya Jammeh
Hoto: picture alliance/AP Photo/J. Delay

 Ana kokari na warware rikicin Gambiya da ke yanki na yammain Afirka shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci wasu shugabanni na kasashen yankin domin wata tattaunawar neman lallashin Yahya Jammeh kan ya amince da kayen da ya sha a zaben da aka kammala a farkon watan Disamban da muke ciki.

Ga Dr Alhaji Farfesa Yahya Abdul Aziz Awal Jemus Junkung Jammeh Nasirudden babili Mansa dai rudani da halin na isa ba bako ba ne cikin mulkinsa na shekareu 22 a 'yar karamar kasa ta Gambiya da ke yankin yammacin Afirka.

To sai dai kuma mai sunayen da suka cika sadara ta rubutu dai na neman sha ta wuce karfi na cikinsa bayan da ya ce ya dawo daga rakiyar sakamakon zaben da ya sha kaye a cikinsa a farkon watan Disamban da muke ciki.

Gambia neuer Präsident Adama Barrow
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Hankali dai ya tashi cikin kasar da makwabta bayan da Jammeh ya ce zaben ya rushe kuma ana bukatar sake shi, a tsakanin kasashen yankin yammacin Afirka da ke tunanin sun iso gaci ga tsari na demokaradiya mai ingancin amma kuma Jammeh ke cewar har yanzu da sauran tafiya.

Ya zuwa ranar yau dai jagoran sauyin yankin na yammacin Africa kuma shugaban tarrayar najeriya na jagorantar wata tawaga ta shugabanni na kasashen yankin guda uku da yanzu haka suka isa Banjul babban birni na kasar domin tattaunawa da ma neman mafitar rikicin.

Gambia Präsidentschaftswahl
Hoto: picture alliance/AP Photo/J. Delay

Duk da cewar ya amsa shan kaye dama alkawarin mika mulki ga masu adawa na kasar dai akwai hasashen wata barazana ga makoma ta shugaban na zaman uwa makarbiya cikin sabuwar takkadamar da a tunanin Dr Jibrin Ibrahim da ke zaman tsohon sakataren gamin gambiza na kungiyoyi na  fararen hular yankin  ECOWAS ke iya rikidewa ya zuwa yaki babba.

Tuni dai Jammeh ya ce kasarsa ta fice daga kotun hukunta manya na laifukan da ke iya kai wa ga tarnaki ga 'yancinsa nan gaba, kafin sabuwar barazanar da a cikinta magoya bayan Adama Barrow ke fadin suna shirin mayar da kasar cikin ikon kotun kuma mai yuwuwa Jammeh na iya fuskantarta nan gaba.