1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Netanyahu na shan suka a cikin gida

Mahmud Yaya Azare
October 24, 2023

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na fuskantar matsin lamba a ciki da wajen kasar kan makomar fursunonin yakin da Hamas ke garkuwa da su,da aka kiyasata sun kai mutum 220

https://p.dw.com/p/4XyrV
Israel | Benjamin Netanjahu im Gespräch mit Soldaten an der Grenze zum Gazastreifen
Hoto: Avi Ohayon/Israel Gpo/ZUMA/picture alliance /

Kasa da mako guda bayan da ta sako wasu Amurka biyu da ta kame a yayin farmakin da ta kai Isra'ila, makonni biyu da suka gabata, kungiyar ta Hamas ta sake sako wasu mata biyu tsoffi 'yan Isra'ila, guda mai shekaru 85 da kuma wata mai shekaru 79 saboda dalilai na rashin lafiya kamar yadda kakakin rundunar Al-Qassam Birgade, ta mayakan Hamas Abu Ubaidah ke fadi

  "Muna rike da fursunonin yaki ne bisa ka'idojin da shari'ar musulunci ta gindaya mana yadda muke jinyar masu raunuka daga cikinsu, muke kuma basu irin abincin da muke ci, mu kwantar da su a irin makwancinmu. Cikin wadanda muka kama, akwai wadanda muke daukarsu a matsayin bakinmu da za mu sako su da zarar lamuran tsaro sun daidaita. Sai dai abin takaici, luguden wuta kan mai uwa da wabi da Isra'ila ke yi a Gaza ya kai ga halaka fursunonin yaki 22 da ke hannunmu.”

Wani Jami'in Hamas Ayman Nofal
Wani Jami'in Hamas Ayman NofalHoto: Ashraf Amra/AP/Zuma/picture alliance

Tuni dai jikokin tsoffin da aka sako suka yi godiya ga wadanda suka taimaka aka soko kakaninnsu musammanma kasashen Qatar da Masar:

Karin Bayani: Hamas ta saki wasu Amurkawa da ta tsare

Wata Dattijuwa 'yar Israila da Hamas ta sako bayan garkuwa da ita
Wata Dattijuwa 'yar Israila da Hamas ta sako bayan garkuwa da itaHoto: Janis Laizans/REUTERS

 "Muna matukar farin ciki da dawowar kakaninmu. Sun fada mana cewa an yi ta dawainiya a inda ake tsare da su. An kuma sanya su karkashin kulawar likitoci da ke basu magungunan da suka saba sha. Muna fata sauran fursunonin da ake tsare da su za su samu damar komawa ga iyalansu.”

Ci gaba da sakin fursunonin yaki da Hamas ke yi dai ya jefa gwamnatin Netanyahu cikin tsaka mai wuya sakamakon matsin lambar da ta ke fuskanta a ciki da wajen kasar.

Ezhaq Bin Sholam mai ba da shawara kan harkokin tsaro a majalisar dokokin Isra'ila,ya ce akwai bukatar a sake lissafi

Karin Bayani: Kokarin sako Isra'ilawa daga hannun Hamas

Mata biyu 'yan Israila da Hamas ta sako bayan garkuwa da su
Mata biyu 'yan Israila da Hamas ta sako bayan garkuwa da su Hoto: Hostages and missing families forum/Handout/REUTERS

"Zai yi matukar wuya, idan muka kaddamar da samame ta kasa mu iya 'yanto dukkanin wadannan fursunonin da ransu ko da lafiyarsu. A ganina a yanzu bayan da muka yi raga raga da Gaza, mun karya lagon kungiyar Hamas, mafi alfanu garemu, mu shiga tattaunawa da wakilan Hamas don fanso fursunoninmu ko musayen fursunoni da kungiyar ta Hamas.”

Duk hakan dai na zuwa ne,a daidai lokacin da kakakin gwamnatin Hamas Salamah Ma'aruf ke cewa, kidiidigar baya-bayan nan ta wadanda hare haren kan mai uwa da wabi na Isra'ila kan zirin Gaza, ya halaka mutane 5,233 da suka hada kananan yara 2,123 a yayin da mata suka kai 2,421 ciki har da likitoci 59 da ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya 27.

Sai dai duk da hakan, wannan bai hana kungiyar ta Hamas ci gaba da harba rokoki kan garuruwan Isra'ila ba, lamarin da ya sanya Amurka tura wa Isra'ila wasu kwarrarru kan dabarun yaki da za su taimaka mata tunkarar kungiyar da ta zama raina kama ka ga gayya.