Isra'ila ta nemi goyon bayan kasashe
October 17, 2023"Dole ne duniya ta goyi bayanIsra'iladon kayar da Hamas," in ji Benjamin Netanyahu tare da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da ke ziyara.
Shugaban gwamnatin Jamus na daya daga cikin manyan 'yan siyasa da suka ziyarci Isra'ila tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 1,400. Harin martanin da Isra'ila ta kai aZirin Gaza kuwa, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 3,000, gabanin shirin Isra'ilar na kai gagarumin hari ta kasa a kan Gaza.
Yayin da yake magana kan yadda 'yan Nazi suka halaka Yahudawa sama da miliyan shida, Netanyahu ya ce kisan gillar da 'yan Hamas suka yi, shi ne laifuka mafi muni da aka aikata a kan Yahudawa tun bayan kisan kiyashin da aka yi musu.
A bangarensa shugaba Olaf Scholz ya zargi Hamas da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa a zirin Gaza mai yawan jama'a, inda mayakan ke rike da mutane 199 da suka kama a lokacin harin da suka kai a kudancin Isra'ila.
Scholz ya ce wajibi ne a kare rayukan fararen hula, kuma gwamnatin Jamus ba zata yi kasa agwiwa ba wajen rage radadin da suke fuskanta.