'Yan Niger Delta sun koka kan rashin ci gaban yankin
January 9, 2019Daruruwan Matasa da suka hada da 'yan bindiga sun fito daga Jahohi tara na yankin Niger Delta inda suka koka cewar, hukumar NDDC bisa Jagorancin Nsima Ekere ba ta tabuka komai ba dangane da ayyukan da suka kamata a rika yi wa yankin. 'Yan zanga-zangar da suka faro tun a ranar Litinin, sun ce za su ci gaba har sai hukumar ta NDDC da kuma fadar shugaban kasa sun ji kokensu.
Jagoran masu zanga-zangar Comrade Tonye Bobbo ya zargi shugabannin hukumar da yin danniya da kuma nuna wariya da Izgilanci. Ya ce wa’adin ‘yan hukumar gudanarwar NDDC din ya kare tun shekarar da ta wuce wanda ya kamata a rush su a nada sabbi.
Sakataren kungiyar ‘yan bindigar Niger Delta da aka yi wa afuwa, Kwamared Karo Edo, ya ce babu wani abin kirki da hukumar ta NDDC ta yi a cikin shekaru uku karkashin jagorancin Nsima Ekere, don haka hukumar ta gaza, musamman ma wajen kulawa da matasan yankin. Matasan dai sun yi zargin cewa akwai ayyuka da dama da aka fara a baya, amma kuma aka yi watsi da su a garuruwan al'ummomin, alhali a garuruwan ake hako mai.