CSC ta soke muhawara a Nijar
February 9, 2021Wannan mataki da Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Kasa a Nijar din wato CSC ta dauka dai, na zuwa ne bayan da dan takarar adawa Alhaji Mahaman Ousmane ya sanar da cewa ba zai halarci maBazoum Mohamedhawarar ba. Tuni kuma 'yan siyasa da ma sauran al'ummar kasar suka soma mayar da martani kan wannan batu. Hukumar ta CSC dai ta shirya gudanar da muhawarar ne a ranar 19 ga wannan wata na Fabarairu tsakanin dan takarar adawa Mahamane Ousmane da kuma na bangaren masu mulki Bazoum Mohamed.
Sai dai da take mayar da martani, jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya wacce dan takararta ya karbi gayyatar muhawarar daga hukumar ta CSC hannun biyu, ta bakin Malam Adamou Manzo ta ce ta san a rina domin a cewarsa dan takarar adawar ba ya da ta cewa a gaban al'umma.
Karin Bayani: Kaddamar da yakin neman zabe
Tuni dai matakin dan takarara adawar na Jamhuriyar Nijar na kauracewa muhawarar ya haifar da mabambantan ra'ayoyi daga al'ummar kasar, inda wasu ke ganin mutuncin da ke da akwai tsakanin 'yan takarar biyu da suka fito daga jiha daya ne, ya sanya dan takarar adawar ya nemi kauce wa duk wani sa in sa a bainar jama'a tsakaninsa da abokin hamayyar tasa wanda kane ne a gare shi ta wani fannin.