Nijar: Horar da matasa kan dimukuradiyya
October 20, 2023Tun da jimawa dai masana da sauran masu lura da al'amura suka gano cewa ba wai dimukuradiyya ce ke kasancewa matsala a kasashen Afirka kamar jamhuriyar Nijar ba, sai dai yadda su masu tafiyar da harkokin dimukuradiyyar ke haddasa cikas ta dalillai da dama kamar son abin duniya ko amfani da mulki don cin zarafin wani dan adawa lamarin da ya sanya duk horon da ake bayarwa ke kasa yin cikakken tasiri. Da yake magana Kaka Touda Mamane Gwani, mai horon matasa a kungiyar Alternative Espace Citoyen, ya ce sun lura akwai matsala ganin cewa akasarin matasan sai a wajen horo ne suke sanin mene ne ka'idojin dimukuradiyya da ma tsarin siyasa, lamarin da ke nuni da cewa akwai jan aiki a gaba:
Karin Bayani: Shawo kan kalubalen dimukuradiyya a Nijar
Lalle idan aka dubi yadda harkokin dimukuradiyya suke gudana a kasa kamar Nijar, inda ga ka'idojin da dimukuradiyya ta shinfila wanda akansu ne yan siyasa ke yin takara amma daga bisani kowa sai ya yi abin da ya ke so.
Matasa dai da dama sun jima suna samun horo kan tafiyar dimukuradiyya, harkokin siyasa da akidoji na nuna kishin kasa wanda kungiyar Altermnative da ma wasu kungiyoyi ke bayarwa, sai dai idan aka dubi yadda matasa da ma wasu yan siyasa ke bi tare da nuna goyon baya idan aka yi juyin mulki abn bai je daidai ba, kuma a cewar Zainabou Mahaman wata matashiyar yar siyasa da ke samun horo ta ce har yanzu da sauran zomo kaba kan batun dimukuradiyya a Nijar:
Babban abin da yanzu ke kara jan hankali wanda ma a ke ganin zai iya kawo sauyi wajen tafiyar dimukuradiyya a nan gaba a kasar Nijar, shi ne yunkurin da sabbin hukumomin mulkin soja ke yi na tsaftace tafiyar tare da kwato kasashe daga karkashin yan mulkin mallaka da ke gama baki da wasu magabata a wasu kasashen na Afirka inda suke karkata akalar dimukuradiyya yadda su suke so ba wai yadda al'ummar kasa za ta ji dadi ta gani a kasa ba.