Karancin likitocin dorin kashi a Nijar
May 9, 2024Kwararrun likitocin dorin sun kuma koka kan rashin sanin makamar aikin mafi yawancin madoran gargajiya wanda ke zama dalilin haddasa nakasa ga mutane da dama da suka samu kariyar da likitan dori na zamani kan iya magancewa ba tare da matsala ba.
Rashin asibitocin kashi a asibitocin Nijar na haddasa cikas a kan sha'anin kiwon lafiya
Lokacin wani taro ne da wararrin likitocin dori na kasar ta Nijar suka shirya a birnin Yamai fadar gwamnatin kasar ta Nijar inda suka yi bitar aikin nasu suka fito da jerin matsalolin da da suka dabaibaye aikin nasu farawa da karancin likitan dori a kasar kamar dai yadda Malama Rayya Harouna kwararrar likitar dori a babban gidan asibitin birnin Yamai ta ce likitocin dori na zamani na bukatar gwamnati da ta gaggauta ta dauki sabbin likitcoin dori da kuma daukar nauyin wani kaso na kudin dori a likita wanda ke tashi daga jika 300 zuwa har sama da 800 na CFA a likitocin gwamnatin kasar ta Nijar.