Turkiyya cikin sababbin kawayen Nijar
July 17, 2024Kasar ta Turkiyya dai, na hulda ne da Jamhuriyar Nijar a fannoni da dama da suka hadar da tsaro da ilimi da fannin gine-gine. Tawagar manyan jami'an gwamnatin kasar Tukiyyan ta kunshi ministan harkokin kasashen waje Hakan Fidan da ministan tsaro Yasar Güler da na makamashi da albarkatun kasa Alparslan Bayraktar da shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasar Tukiryyan Ibrahim Kalin da sakataren Masana'antun Tsaro Haluk Görgün Kimdir da kuma mataimakin ministan kasuwanci Ozgur Volkan Agar. Kuma za a iya cewa bayan ziyarar mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Turkiyya a watan Nuwambar bara a Nijar din, wannan ita ce ziyara ta farko da wasu manyan jami'an kasar Turkiyyan suka kawo tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin bara. Bangarorin biyu dai sun tattauna batutuwa da dama, wadanda suka shafi dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Da yake jawabi yayin soma tattaunawar tasu dai, ministan harkokin kasashen wajen Nijar Boukari Yaou Sangare ya yaba da huldar da ke tsakanin kasashen biyu. A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar ta Turkiyya Fidan Hakan ya ce yanzu lokaci ne da ya kamata a karfafa hulda ta dangantaka tsakanin kasashen biyu da suka kasance aminan juna. A cewar firaministan Nijar din Ali Mahaman Lamine Zeine wanda kuma shi ne ministan kudi na kasar, girman wannan tawaga ya nuna karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu karara. An dai kafa kwamitoci har guda uku, domin samun tataunawa mai armashi a fannoni dabam-dabam da suka hadar da na ministocin harkokin waje da na tsaro da zai duba batutuwa na diflomasiyya da tsaro. Akwai kuma kwamitin ministocin makamashi da man fetur da kuma kwamitin ministocin kasuwanci, inda dukanninsu za su dukufa domin samar da kyakkyawar al'kibla wajen karfafa hulda tsakanin kasashen biyu.