Nijar: An fara koyar da harshen Rashanci a cikin makaratu
April 9, 2024Dalibai kimanin 25 ne maza da mata ke zama rukunin farko na daliban jami'ar ta birnin Yamai da suka yi rijista ke koyon harshen Rashanci a sabuwar cibiyar koyon wannan harshen da ke zama irinta ta farko a kasar. Kuma wasu daga cikin daliban sun bayyana farin cikinsu da tsarin da kuma burin da suke son cimma a cikin koyon harshen
Tawaga ta musammun ta zo dagá Rasha domin girka sashen koyon Rashanci a cikin makarantu
Tawaga ce dai ta musamman daga jami'ar patrice Lumumba ta birnin Moscou ta iso a kasar ta Nijar domin kaddamar da wannan cibiya ta koyar da harshen Rashanci a jami'ar Abdoulmoumouni ta birnin Yamai. Parfesa Khabiba Shagbanova ta jami'ar Moscou kana shugabar sashen kula da huldar harkokin ilimi tsakanin Rasha da Afirka ita ce jagoran tawagar. '' Bude cibiyar koyar da harshen Rashanci na taimaka wa ga karfafa huldar kasashenmu biyu a fannin raya al'adu da ilimi. Sati biyu kenan da muka zo nan , mun yi nasara samun dalibai masu yawa da ke da sha'awar koyon Rashancin. Yanuzu haka akwai kamar dalibai 25 maza da mata da ma malamansu wadanda suka yi rijista a sashen koyon Rashanci.