1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kotun koli ta ja kunnen 'yan siyasa

Gazali Abdou Tasawa
December 18, 2020

A Jamhuriyar Nijar 'yan siyasa da masu fafutikar kare Demokradiyya suna tofa albarkacin bakinsu dangane da kashedin da kotun tsarin mulki ta yi ga masu suka lamirin hukunce-hukuncen da take fitar

https://p.dw.com/p/3mvZJ
Verfassungsgericht in Niamey Niger
Hoto: DW/M. Kanta

A cikin wata sanarwa da ta fitar kotun tsarin mulkin kasar ta Nijar ta yi kashedi ga 'yan siyasa na kowane bangare da ma sauran rukunnan al’umma da ke sukar lamirin hukunce-hukuncen da ta ke yanke wa a game da karrarakin da ake shigarwa gabanta na kalubalantar wani dan takara. Kotun ta yi zargin cewa wata makarkashiya ce da wasu suka tsaro da nufin bata mata suna da haddasa hasuma a cikin kasa yadda daga karshe za su dora alhakin duk matsalolin da za a fuskanta a zaben akan hukumomin kasar da kuma musamman kotun tsarin mulkin. Abdoukadri Umaru Alpha daya daga cikin 'yan takarar neman kujerar shugaban kasa kana daya daga cikin wadada suka shigar da kara a gaban kotun kolin kan sahihancin takardun zama dan kasa na  Bazoum dan takarar jam’iyya mai mulki ya ce bai kamata ba ta dunga biye wa irin wadannan cecekuce da ke biyo bayan hukunce-hukuncen nata.

Kotun tsarin mulkin dai ta yi barazanar  cewa daga yanzu za ta dauki matakin ladabtarwa a kan duk wanda ta samu yana sukar lamirinta. Sai dai ko baya ga 'yan siyasa ana samun masu yin tawili kokuma ma kai tsaye suna nuna rashin amincewarsu da hukunce-hukuncen da kotun ke fitarwa a baya bayan nan kan batun zabe. Malam Gamache wani dan fafutika a Nijar ya ce ba abin da suke jira daga kotun illa ta yi masu adalci.

To sai dai daga nashi bangare Malam Dambaji Son Allah shugaban kawancan kungiyoyin farar hula na ROUAD na ganin rashin sirri da kotun ba ta da shi a yanzu shi ne ya haifar mata da wannan raini ga wasu 'yan kasa. Ko a baya bayan nan ma dai kotun tsarin mulkin ta yi watsi da karar da wasu 'yan takara suka shigar a gabanta suna masu kalubalantar sahihancin takardar zama dan kasa ta Bazoum Mohammed.

Abin jira a gani ia nan gaba shi ne tasirin da kashedin da kotun ta yi zai yi wajen hana 'yan kasa ci gaba da sukar lamirin hukunce-hukuncen da ta ke yanke wa a harkokin zabe a kasar