Tandja Mamadou: Zaman makoki a Nijar
November 25, 2020Koke-koke ya barke a gidan marigayi Tandja Mamadou bayan rasuwarsa, inda daruruwan jama'a kama daga 'yan siyasa zuwa 'yan farar hula da kuma 'yan uwa da abokan arziki da sauran talakawa, na ta cincirindo zuwa gidan marigayin da ke birnin Yamai fadar gwamnatin kasar, domin isar da gaisuwar ta'aziyya ga iyalansa. Wasunsu kuma sun bayar da shaida a kan yadda Tandja ya tafiyar da salon mulkinsana a cikin kaunar talakawa.
Karin Bayani: Shekaru 10 bayan kaddamar da juyin mulki
'Yan Nijar da dama ne dai ke kallon Tandja Mamadou a matsayin jarumin shugaba kuma dan kishin kasa, sakamakon wasu matakai na tarar aradu da ka da ya rinka yi domin ci-gaban Nijar. Sai dai ba wai 'yan kasa ne kadai ke kallon Tandja a matsayin Jarumi ba, hatta iyalansa sun tabbatar da hakan dangane da yadda ya yi kasadar kalubalantar Amirka, a kokarinsa na ganin Nijar ta soma hako man fetur dinta.
To sai dai duk da rawar da tsohon shugaban ns Nijar Tandja Mamadou ya taka wajen kafa tubalin ci-gaban da Nijar ta samu a fannin tattalin arziki a yanzu, wasu na zarginsa da bata rawarsa da tsalle bayan da ya yi tazarce a karshen mulkinsa, wanda ya yi sanadiyyar da sojojin kasar suka kifar da gwamnatinsa. To sai dai da yake mayar da martani a kan wannan batu, Malam Moktar Kasum kakakin gwamnati a lokacin mulkin Tandja ya ce Tandja ya yi tazarcen ne da kyakyawar niyya.
Karin Bayani: Sakin Mamadou Tandja ya samu martani
Za dai a kararram marigayin a fadar shugaban kasar Jamhuriyar ta Nijar, saboda gudunmawar da ya bayar gabanin gudanar da jana'izarsa a ranar Alhamis 26 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki a garin Maine, kamar yadda marigayin ya yi wasiyya. Tuni kuma gwamnati ta bayar da jiragen sama guda biyu wadanda za su jigilar iyalansa da sauran mutanen da za su halarci jana'izar tasa, a garin na Maine da ke cikin jihar Diffa.