1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Ambaliya ta mamaye hanyoyi da gidaje

Salissou Boukari AH
August 22, 2024

A Jamhuriyar Nijar masu aikin gyaran hanyar da ta katse da ta raba birnin Yamai da sauran jihohin kasar sun yi nasarar cike babban gibin da ruwa ya haddasa.

https://p.dw.com/p/4jnnq
Kennedy-Brücke über den Fluss Niger, Afrika
Hoto: picture-alliance/dpa

 Motocinkwasar tsakuwa da duwatsu ne dai kimanin 24 na kamfanin SATOM mai kula da yin hanyoyi da gyaransu suka kasance cikin wannan aiki ba dare ba rana inda suna kwaso manya-manyan duwatsu shi kuma mai dan dankao yana bajewa har suka kai ga cike wannan wagegen gibi na wajen mita 230 da ruwan suka haddasa wnda al’umma masu bulaguro suka kasance tun daga ranar Lahadi da ta gabata ba gaba ba zuwa ba dawowa.

Nigeria Fluß Niger
Hoto: Patrick Meinhard/AFP/Getty Images

Da yake magana kan wannan batu, mai garin na  Sonrey Ganda Alhaji Ibrahin Daouda Mokaina,ya ce lamarin sai hamdala tun da aka kai ga dinke wannan babbar baraka, sai dai akwai tausayi ga wadandan suka shafe kwanaki ta sabili da wannan matsala. Adamou Idrissa Sorey wanda shi ma katse hanyar ya hana shi zuwa wajen iyalinsa daga wannan bangare zuwa wancan ya ce babu abin cewa sai godiya ga Allah. Sai dai daga bisani jagoran wannan aiki na gyaran hanyar da ta katse Issa Djibo ya yi fatan ganin jama’a za su bi wannan hanya cikin nutsuwa a nan  gaba.