Damagaram: Matsalar satar amfanin gona
August 21, 2024Sakamakon girman da wannan matsalar ta sace amfanin gona a jihar ta Damagaram, tuni sarakunan gargajiya a karkara suka bukaci hukumomi da su dauki matakan da suka dace ganin yadda danyen wake da ake kira gajanga ya fara yawa a kasuwannin cikin gari. Ita dai wanan matsala ta satar kayan gona a irin wanan lokaci na farkon nunar amfanin gona, tsohuwar matsala ce ga manoman yankin Damagaram musaman masu makwabtaka da babban birnin. To sai dai a bana kasancewar shekara ba ta yi gadon shekara ba, a cewar manoman da abun ya shafa da suka ce ya wuce kima. Barayin dai na cire tushiyar gaba daya ta amfanin gonar da suka hadar da gurjiya da wake da a yanzu suka fara 'ya'ya. A yayin da manoman ke kokawa da wanan matsala ta sace-sacen amfanin gona, yawaitar albarkatun noman na bana a kasuwa da wuraren sayar da kayan lambu ta tilasta manoman zargin masu shigo da sabuwar cimakar kasuwa ba nomansu ba ne. Rohotanni daga wasu yankunan kananan hukumomi na cewar tuni an fara cafke masu aikata wannan danyan aiki a gonakin manoma, inda ake fatan hakan ka iya rage kaifin matsalar.