Nijar: Sojoji sun ki cewa komai kan dage takunkumin ECOWAS
March 1, 2024Yanzu haka dai a yayin da wasu ‘yan kasar ke ganin dacewar shirun magabatan nasu kan wannan batu, wasu na ganin matakin cire takunkumin ya zame wa mahukuntan tamkar wani karfen kafa ga makomar mulkin na su.
Kwanaki shida kenan dai da a kwana a tashi da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta CEDEAO da ta kasashen masu tsarin kudin bai day na CFA wato UEMOA suka cire wa kasar ta Nijar jerin takunkuman kariyar tattalin arzikin da suka saka wa kasar a sakamakon juyin mulkin watanni sama da bakwai da suka gabata.
Sai dai har kawo yanzu hukumomin mulkin sojan kasar ba su fito suka bayyana matsayarsu a kai ba, inda hatta gidan rediyo da talabijin na kasa bai taba kawo zancen ko miskala zarratun ba. Lamarin da ya soma haifar da rudani tsakanin ‘yan kasa wadanda ke dora ayoyin tambaya kan dalilin mahukuntan kasar na yin biris da wannan batu.
Karin bayani: Benin: Martani daga 'yan kasuwar Nijar
To amma Malam Bana Ibrahim dan fafutika mai goyon bayan mulkin sojan kasar ya ce babu dalilin mahukuntan kasar na yin wani furuci ga batun ECOWAS wacce tuni kasar ta fice daga cikinta.
Ga Malam Abdoulkader Maidalili, da Malam Alassan Intinikar dukkaninsu masu adawa da mulkin sojan na ganin cire takunkumin ECOWAS din na zama tamkar wani tarnaki ga wani agendar boye da sojojin suke da shi.
Karin bayani: Nijar: Ba ta sauya ba a kan iyakokin kasar
Sai dai Malam Soumaila Amadou Awaiwaya dan siyasa a Nijar, na ganin ala kulli halin, akwai bukatar mahukuntan sojin kasar su fito su bayyana wa ‘yan kasa matsayarsu kan matakin na ECOWAS.
Daga nashi bangare dai ministan harkokin wajen Mali abokin kawancen kasashen AES tare da Nijar, ya bayyana cewa babu wani furuci da za su yi kan matakin kungiyar ta ECOWAS kungiyar da basa a cikinta.