1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar ta bude kofofin cinikayya da arewacin Afirka

Gazali Abdou Tasawa M. Ahiwa
January 2, 2024

Nijar ta kuduri aniyar karfafa cinikayya da Aljeriya da Libiya da Maroko ta yadda za ta yi amfani da tashoshin ruwan kasashen domin shigo da kayayyaki daga ketare ko kuma fitar da kayan kasar.

https://p.dw.com/p/4aoHG
Tashar jiragen ruwa ta kasar Maroko
Tashar jiragen ruwa ta kasar MarokoHoto: Chen Binjie/Xinhua/picture alliance

Aniyar gwamnatin ta Nijar na zuwa ne a daidai lokacin dakasar ke kaurace wa shigo da kaya ta tashar ruwan Cotonou da ke zama mafi kusa ga kasar. Sai dai a daidai lokacin da kungiyoyin ‘yan kasuwa ke lale marhabin da shirin, masana harkokin tattalin arziki na ganin akwai bukatar yin taka tsantsan a cikin lamarin.  

Tun dai bayan da matakin takunkumin tattalin arzikin da kungiyar ECOWAS ta saka wa Nijar saboda juyin mulki sojoji uska yi a bara, wanda ya yi dalilin gazawarta wajen shigo da kayayyaki ta tashar ruwan Cotonoun Jamhuriyar Benin da ke zama tashar ruwa mafi kusa ga Nijar.

Mahukuntan Nijar din sun dukufa wajen lalibo sabbin hanyoyin sauwaka shigo da kaya a cikin kasar ko fita da su zuwa ketare. A kan haka ne bayan tashar ruwan Lome ta kasar Togo da Nijar ke amfani da ita, gwamnatin kasar ta sanar da shirin soma amfani da tashoshin ruwan Aljeriya da Libiya da Maroko a wannan aiki.

Gwamnatin kasar ta Nijar ta kuma sanar da shirin sabunta ilahirin yarjeniyoyin cinikayya da na hakar ma’adinai da kamfanonin ketare da suka hada da na ma’adanan.

Yanzu dai ‘yan Nijar sun zura ido su ga yadda gwamnatin kasar za ta soma aiwatar da wannan aniya tata ta soma aiki da tashoshin ruwan kasashen Larabawa na arewacin Afirka da kuma sabunta yarjeniyoyin ayyukan hakar ma’adanai a kasar