Nijar: Zargin hana 'yan adawa yada manufofinsu
January 14, 2016Kawance 'yan adawar na Nijar ya ce wannan matakin da gwamnati mai ci a Nijar din ta dauka abinda bai dace da tsarin dimokradiyya ba ne har ma kakakin kawance Madam Bayard Hajiya Mariama Gamatche ta ce yin hakan daidai ya ke da ''mulkin kama karya ne''. 'Yan adawar dai suka ce wannan yanayi da aka shiga ya sanyasu yanke shawarar amfani da kafafen yada labarai masu zaman kansu duk kuwa da rashin nisan zangon da suke da shi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da kawancen 'yan adawar kasar ya koka da yanda ake nuna masa rashin adalci wajen wallafa wasu tarurukan su na siyasa ba musamman ma a wannan karon da zabukan game gari ke kara karatowa, har ma su ke cewar matakin na daga cikin take-taken murkushe demokradiya ne ta hanyar nuna banbanci tsakanin 'yan siyasa a kasar ta Nijar.
Suma dai gungun kawancen jam'iyyun da ke a matsayin 'yan baruwanmu sun jima su na kallo da ma fuskantar wannan matsalar, sai dai a dan tsakanin nan sun fara yin matsin lamba ga gwamnati na ganin an basu dama kasancewa zabe na kara karatowa. Alhaji Lawal Magaji da ke takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar Adalci Mutunci ya yi kira ga hukumomin da su sauya tafiya.
Gwamnatin Nijar din a nata bangaren ta bakin ministan yada labarai Yahouza Sadissou Madobi nisanta gwamnatin ya yi da wannan batu inda ya ke cewar lamari ko kusa ba haka ya ke ba don kuwa hukumomi na bada dama daidai wa daidai ga kowa da ke son yada manufarsa a kowacce kafa ta gwamnati.