Likitocin Najeriya sun shiga yajin aiki
April 2, 2021Wannan yajin aiki dai, ya jefa aikin kula da lafiya cikin mawuyacin hali a Tarayyar Najeriyar a daidai lokacin da ake yaki da cutar COVID-19 da ma aikin allurar rikag-kafin cutar. Yajin aikin da likitocin Najeriyar suka shiga a karkashin kungiyarsu ta likitoci masu neman kwarewa, wadanda sune kashi 40 cikin 100 na yawan likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati, ya nuna cin tura da rushewar duk wani kokari da gwamnatin kasar ta yi na shawo kan likitocin su yi hakauri.
Karin Bayani: Yajin aikin likitoci ya ta'azzara lamura a Najeriya
Likitocin dai na korafi ne a kan abin da suka kira gazawar gwamnati na mutunta yarjejeniyar da suka cimma da ita, a kan batun albashi da kudin alawus-alawus da ma karancin kayan aiki. To sai dai duk da kokarin cimma matsaya abin ya ci tura. Koda yake gwamnatin Najeriyar dai, a karkashin jagorancin ministan kwadago da ingantuwar aiki na kasar Dakta Chris Ngige ta bayyana cewa tana kokarin shawo kan wannan matsala.
Suna dai wannan yajin aikin ne a daidai lokacin da Najeriyar ke yaki da cutar COVID-19 a kasar da ma aikin riga-kafin cutar da aka kwashe kusan wata guda da farawa, amma har yanzu mutane dubu 800 aka yi wa daga cikin alluara milyan hudu da aka bai wa kasar.
Karin Bayani: Yajin aikin likitoci a Adamawa da ke Najeriya
Akwai tsoron yadda wannan yajin aiki zai iya shafar yaki da cutar. Likitocin Najeriyar dai sun dade suna shiga yajin aikin da ke gurgunta aikin samar da lafiya ga al'ummar kasar, domin Najeriyar na da likitoci sama da dubu 40 kuma likitoci dubu 16 na karkashin kungiyar likitoci masu neman kwarewa ne a kasar, wadanda suka shiga yajin aikin na sai abin da hali ya yi.