NLC na adawa da yunkurin kafa sabon tsarin albashi
March 10, 2021Dubban ‘ya'yan kungiyar kodagon Najeriya ta NLC sun ta rera takensu a lokacin da suka yi tattaki tun daga dandalin ‘yanci da ke Abuja har zuwa majalisar dokokin Najeriyar inda suka yi zanga –zangar lumana. Abin da ke ci musu tuwo a kwarya dai, shi ne kudurin dokar da aka gabatar wa majalisar dokokin kasar, a wani yunkuri da wasu gwamnonin kasar ke yi don ganin an cire tare da kakkabe batun karin albashi daga ikon yin doka daga majalisar kasa ya zuwa jihohi, ta yadda za su yi yadda suke so tare da bai wa jihohi damar yin gaban kansu.
Comrade Ayuba Waba, wanda shi ne shugaban kungiyar kodagon Najeriya ya ce: " Ba za mu amince da shi ba domin kundin tsarin doka na ma'aikata na duniya ne ya tanadar da doka, wanda dole ne a kasashen duniya a samu mafi karancin albashi domin kar da a maida ma'aikata bayi."
An ta kai ruwa rana da ja-in ja na nuna rashin amincewa da kalaman da wakilan majalisar suka rinka yi daga 'y'ayan kungiyar kodagon da suka rinka ihu suna katse jawaban da ake yi. Hon Alhassan Ado Doguwa wanda shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar tarayya, ya yi wa masu zangar jawabi inda ya shaida matakin da za su dauka. Ya ce " Kudiri ne, bai zama doka ba har yau. Za mu sake ba su dama a kwamitin da ke kula da canje-canje na tsarin mulkin Najeriya wanda wannan kudiri yake neman ya je gare shi:"
Amma mene ne hatsarin wannan mataki na kudurin doka da 'ya'yan NLC ba su yarda da shi ba ? Comrade Nasiru Kabiru wanda ke zaman jigo a kungiyar kodagon Najeriya ya ce: "Idan wannan abu ya koma hannun gwamnoni, dubu biyar wasu za su rika biyan ma'aikata don za su ce ba su da kudi." .
Akwai mata da yawa da suka shiga wannan gwagwarmaya ta zanga-zangar lumana da suma suka yi tattaki. Comrade Hafsat Shu'aibu ta kungiyar kodago ta TUC ta ce: "Muna so a kashe wannan abin domin idan ya zama doka, mutanen kasar nan za su sha wahala gurim biyan albashi."
Da alamun dai 'ya'yan kungiyar sun sha damara ta ci gaba da fito- na- fito a kan batun albashi a dai dai