1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yan kwadago na barazanar yin yajin aiki

Uwais Abubakar Idris RGB
June 4, 2023

Kungiyar kwadagon Najeriya ta bai wa gwamnatin Shugaba Tinubu wa'adin janye matakinta na cire tallafin mai ko kuma ta tsunduma yajin aiki.

https://p.dw.com/p/4S8Nc
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed TinubuHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

A Najeriya, majalisar zartaswar Kungiyar kwadago NLC ta kammala wani taro a Abuja inda ta bai wa gwamnatin kasar wa'adin mako guda a maido da tallafin man fetir ko kuma kungiyar ta tsunduma cikin yajin aiki daga ranar 7 ga wannan watan na Yuni.

Taron Kungiyar kwadagon da ya hada da dukkanin sauran kungiyoyin kwadago da ke karkashinta, sun dauki lokaci mai tsawo suna tattauna a kan wannan batu na janye tallafin man fetir da gwamnatin ta yi, inda suka nuna bacin ransu kan cewa an janye tallafin tun ma kafin kudin da aka kasafta don tallafin su kare, wadanda gwamnatin da ta gabata ta samar har zuwa karshen watan nan na Yuni.

Yan Najeriya na fama da matsalar karancin man fetir
Yan Najeriya na fama da matsalar karancin man fetirHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Kungiyar da a baya ta sha nanata adawarta a kan dailai na janye tallafin da gwamnatin kan bayar a Najeriyar, ta bai wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu wa'adi a kan lamarin. Tuni kungiyar kare hakkin jama'a ta Najeriyar ta shiga cikin lamarin na janye tallafin saboda halin da ya jefa al'ummar kasar.

Kungiyar NLC na barazanar shiga yajin aiki
Kungiyar NLC na barazanar shiga yajin aikiHoto: dapd

A baya dai Kungiyar Kwadagon ta yi amfani da yajin aiki da ya zame mata makami na bayyana bacin rai a kan wannan lamari. Amma ga Comrade Isa Tijjani ya ce, dole ne Kungiyar Kwadagon ta jagoranci jama'a ko kuma su waklici kansu.

An tsara cewa, Kungiyar NLC za ta ci gaba da tattaunawa da gwamnati a ranar Lahadin nan. Duk da dagewa da gwamnatin ke yi a kan dole a cire tallafin man fetir saboda matsalar cin hanci da ake da lamarin, kwararru na nuna gazawa na yakar masu wannan hali inda a dalilai na ‘yan tsirarun masu halin bera aka barsu suka jefa alumma fiye da miliyan 200 cikin wahala duk da arzikin mai da Najeriyar ke da shi a yanayi na ga koshi ga kwanan yunwa.