1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nnamdi Kanu na son komawa Birtaniya

Abdul-raheem Hassan
September 8, 2021

Shuguaban haramtacciyar kungiyar Biyafara mai neman ballewa daga Najeriya Nnamdi Kanu, ya kalubalanci gwamnatin Najeriyar da hukumomin tsaro a kotu bisa zargin kama shi daga kasar Kenya zuwa Najeriya ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/404r1
Nigeria Biafra Separatist Nnamdi Kanu
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Karar da lauyoyin shugaban IPOB suka gabatar a wata kotu a jihar Abia da ke Kudu maso yammacin Najeriya, na cewa gwamnati da jami'an tsaro sun take hakkin dan Adam na tsare Nnamdi Kanu, tare da cewa yakamata Najeriya ta fara neman izinin tsare Kanu daga gwamnatin Birtaniya. Lauyoyin sun gabatar da bukatar su ga kotu na neman ba wa shugaban IPOB din izinin komawa Birtaniya.

Nnamdi Kanu wanda ke da fasfo na aksar birtaniya kuma ya ke tsare a Najeriya, ya shafe shekaru biyu a gidan yari, amma ya gudu bayan da kotu ta ba da shi beli a watan Afrilun 2017, sai dai ya sake shiga hannu a watan Yunin 2021 inda yake fuskantar shari'a kan cin amanar kasa da sauran laifuka.