1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NNPC: Corona ba za ta karya arzikin Najeriya ba

March 20, 2020

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, na fatan duk da faduwar farashin mai a kasuwar duniya kasar za ta ci gaba da samun biyan bukata daga fetur.

https://p.dw.com/p/3Zo04
Nigeria Selbstmordanschlag 28.07.2014
Hoto: Reuters

Duk da cewar dai sai  karshen wannan wata na Maris ne ake shirin ganin wani yunkuri a bangaren  kungiyar OPEC  mai kula da hada-hadar man fetur a duniya,  daga dukkan alamu kamfanin man Najeriya na NNPC na ganin mafita a cikin rikicin da ya kalli asarar sama da rabi na farashin da kasar tai kasafi kudinta kansa.

Kawo ranar Juma’ar nan dai farashin gangar man fetur  na a tsakanin Dalar Amirka 24  zuwa 27 abin da ke nufin asara ta kusan Dala 30 kan kowace ganga da tarayyar Najeriya ke fatan na iya sauya makomar kasar da ke neman girma.

To sai dai kuma daga dukkan alamu har yanzu gwiwa ta kamfanin man NNPC na a tsaye a cikin neman mafitar rikicin da ke zaman irinsa na farko a shekaru kusan 20 da suka gabata.

Shugaban kamfanin na NNPC, Mele Kyari, dai ya ce tuni sun nisa wajen samar da dabarun da ke da zummar rage farashin da kasar ke hakar man fetur da kuma samar da kasuwa mai sauki ga man kasar.

‘’Ban ce babu barazana ba, cewa nayi za a samu sauki. Abin da za ayi shi ne a rage kudin da ake kashewa, a kara yawan man da ake hakowa. Bayan haka ana iya cin bashi a gyara hali idan aka shiga irin wannan yanayi. A saboda haka a karshe dai zamu tabbatar da gwamnati bata shiga wata matsala da za ta gagara ba.’’ inji Kyari

Shelkwatar Kamfanin Man fetur na Najeriya NNPC da ke Abuja
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Sai dai ga Abubakar Ali wani masanin tattalin arziki a Najeriya dogaro a kan man fetur da Najeriya keyi ba abu ne mai kyau ga tattalin arzikinta ba.

‘’A Najeriya mun kai wani hali da ya kamata mu samu kudin shiga musamman bangaren noma da kuma ma’adinan cikin gida, mu daina dogaro a kan man fetur. Muna bukatar a bunkasa harkar ilimi yadda matasanmu za su sanya iliminsu wurin fito da abubuwa na ci gaban kasa. Coronavirus annoba ce amma ya kamata ta zamar mana darasi yadda zamu fara dogaro da ma’adinanmu na gida’’ inji Ali

Najeriya dai na zaman daya a cikin kungiyar kasashen OPEC da ake hako mata man fetur a  farashi mai tsada, sabanin kasashe irinsu Saudiyya da farashi na hakar man yake arha sosai.