NNPC zai ja da baya daga mamaye fagen man Najeriya
June 1, 2023Talla
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da kamfanin ya rubanya farashin litar man fetur a gidajen mai mallakar kamfanin.
Sai dai a tattaunwarsa da wani gidan talabijin a kasar, shugaba kamfanin Mele Kyari ya ce nan ba da jimawa ba farashin zai sauko idan aka sami wasu kamfanoni da za su shiga a dama da su wajensamar da man.
Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar, a lokacin rantsar da shi cewa gwamnati ta dakatar da tallafin man fetur.
Wanda tun bayan wannan furuci na sabon shugaban ne aka fara samun dogayen layi a gidajen sayar da mai a daukacin kasar.