1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Obasanjo ya goyi bayan Peter Obi

January 2, 2023

Tsohon shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ya fitar da wata wasikar da a karkashinta ya ke goyon bayan dan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi domin ya gaji Buhari.

https://p.dw.com/p/4LeKa
Nigeria Bildergalerie Staatspräsidenten Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun ObasanjoHoto: Chung Sung-Jun/Getty Images

Ya dai kusan zama al'ada aike wa da wasika, kuma ya rubuta a bisa batutuwa da daman gaske. To sai dai kuma wata sabuwar wasikar ta siyasa a bangare na tsohon shugaban tarayyar najeriyar chief olusegon Obasanjo na neman yamutse hazo na siyasa ta kasar yanzu.

Obasanjon da ya dauki ranar farko a sabuwa ta shekarar dai ya fito a bainar jama'a wajen nuna goyon bayansa ga Peter Obi da ke zaman dan takara na jam'iyyar Labour a zaben da ke shirin ya gudana.

Tsohon shugaban kasar da ya ce ya hada lissafi, ya bai wa matasa na kasar shawara ga zaben Obin a matsayin mutumin da ya ke yi wa kallo irin na Musan da ya ke iya ceto ga kasar da ta share shekaru bakwai da doriya a hannun fir'auna. To sai dai kuma tun ba'a kai ga ko'iba ba dai wasikar na neman dagun hakarkari cikin fage na siyasa ta kasar da hankali ya yi nisa a rabe.

Dan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi
Dan takarar jam'iyyar Labour, Peter ObiHoto: Gbemiga Olamikan/AP/picture alliance

Farin jinin cikin gida ko kuma kokari na tada hayaki, in har masu tsintsiyar na da tunanin ko oho, ga 'yan labour da ke ta tsallen murnar goyon bayan da ke zuwa sau daya a shekaaru guda hudu dai na iya sauya da dama cikin fage na siyasa ta kasar.

Kokari na talar na kwarai, ko kuma dunkunkuno na siyasa dai, yan kwanakin dake tafe na da tasirin gaske ga daukacin makoma ta kasar ko bayan batun siyasar mai zafi. Batu na siyasa, Obasanjo na kokari na kare muradi a tarayyar Najeriyar da ke kama da saniyar tatsar 'yan boko na kasar.

Abun jira a gani dai na zaman daukar wa'azi na shugaban a bangare na matasan da ke tsakiyar cikin ruwa, kuma ke shirin kama takobi da nufin neman tsira.