1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obi ya lashe zaben shugaban kasa a Lagos

Abdullahi Tanko Bala
February 27, 2023

A Najeria sannu a hankali ana samun karin sakamakon zaben shugaban kasar mafi yawan al'umma a Afirka duk da korafin jinkiri da damuwa da suka dabaibaye zukatan al'umma.

https://p.dw.com/p/4O2Dk
Peter Obi, Bola Tinubu a tsakiya, sai kuma Atiku Abubakar
Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Mutane kusan miliyan 90 suka kada kuri'unsu domin zabar wanda zai maye gurbin shugaban kasar Muhammadu Buhari.

A Jihar Lagos dan takarar shugabancin kasa na Jam'iyyar Labour Peter Obi wanda takararsa ta ja hankalin matasa ya lashe zaben shugabancin kasar a jihar Lagos da kuri'iu 582,454 tazara kalilan kan abokin hamaiyarsa na Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu kuma tsohon gwamnan jihar Lagos wanda ya sami kuri'iu 572,606

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar na babbar Jam'iyyar adawa ta PDP ya sami kuri'iu 75,750 a zaben shugaban kasar a jihar ta Lagos.