Peter Obi ya yi ba zata a jihar Lagos
February 27, 2023Mr Peter Obi na jamiyyar Labour Party ya lashe zaben a jihar lagos inda ya kada Bola Ahmed Tinubu dan takarar jamiyyar APC mai mulki a kasar a jiharsa inda ya taba rike mukamun gwamna. Jihar ta kasance tungar jam'iyyar APC mai mulki wadda take rike da kujerar gwamnan jihar yanzu haka.
Karin Bayani:Adamawa: Fargaba kan sakamakon zabe
Mr Shi dai Peter Obi ya samu kananan hukumomi 9 da kuri'u 582,664 yayin da Bola Tinubu ya samu kuri'u 541,850 da kananan hukumomi 11. A gaba daya na sakamakon da akla samu Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki ke kan gaba yayin da Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke mara masa baya, kana Peter Obi na jm'iyyar Labour Party ta ma'aikata ke mataki na uku, amma sakamakon zaben na jihohi kalilan aka bayyana daga cikin jihohin Najeriya 36.
Ko shakka babu har kawo yanzu jama'a a Lagos na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu bisa wannan nasara ta Obi. Madam Chika Nweze tana cewa cike take da farin ciki bisa wannan nasara domin Obi na mutane ne a kasar baki daya. Shi kuwa Mr Prince Adebowale yana cewa wannan nasara ta zo ba zata a cikin Lagos baki daya sai kuma dakon abin da sauran jihohi za su haifar. Shi kuwa Habila Akawu cewa ya yi ba girin-girin ba ta yi mai saboda akwai sauran aiki inda aka duba yawan Najeriya da sauran sakamakon da ake jira na jihohin kasar.
Jihar Lagos ta kasance cibiyar kasuwancin Najeriya kuma daya daga cikin birani mafiya girma a nahiyar Afirka baki daya.