Najeriya: Osinbajo na neman yin takara
April 11, 2022Ya zuwa yanzu dai akalla manya na 'yan siyasa ta kasar guda Bakwai ne dai suka ayyana niya ta takara cikin jam'iyyar APC mai mulkin tarrahyar Najeriya.To sai dai kuma mafi dauka ta hankali na zaman mataimaki na shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo da ya baiyana burinsa na tsayawa takara a zaben na 2023.Cikin wani jawabi na mintuna guda shida ta kafar sada zumunta ta Twitter dai, Osinbajo ya ce yana da niyyar dorawa bisa jeri na ayyuka na shugaban kasar in har ya yi nasarar gado ga Buhari.“Na zauna da 'yan kasuwar da ke cikin harka ta fasaha ta zamani a Legas da Edo da Kaduna. Na zauna da 'yan wasan kwaikwayo na Nollywood da Kannywood da mawakanmu da ke Legas da kano da Onitsa. Na yi magana da manya da kanana na masu kasuwarmu na tsaya inda suke tsaye, na kuma zauna inda suke zaune. Na san fatansu, na san burinsu da ma tsoronsu. Kuma na yi imani za mu iya kai ga bukatu da fatan na al'uma domin kara ciyar da Najeeiya zuwa gaba.To sai dai kuma ko ya zuwa ina kwarewa ta mataimaki na shugaban kasar take shirin ta kai wajen biya ta bukata dai, Osinbajon dai na da jan aikin burge da dama walau a sashen kudancin kasar in da mafi yawa na abokan takun sakar nasa ke da buri iri guda, ko kuma sashen arewacin kasar da ke kallon tsaf ya zuwa yanzu.
Ana jiran ganin yada za ta kasance ko Buhari zai amince da takarar mataimakinsa
Abun jira a gani dai na zaman takarar osinbajon a yankin kudu maso yammacin kasar na kabilar yarabawa da ke shirin fuskantar barazanar rabuwar kai a karon farko tun bayan rikicin NPN da 'yar uwarta UPN shekaru 40 can baya.