1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Osun: Jam'iyyu sun zargi hukumar zaben Najeriya

September 28, 2018

'Yan adawa a Najeriya, sun ce akwai alamun yi masu magudi a zaben gwamnan jihar Osun da ke kudancin kasar da aka kammala.

https://p.dw.com/p/35cDc
Nigeria Präsidentschaftswahl 2015
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Jam'iyyun adawa a Najeriya sun zargi hukumar zaben kasar INEC da kokarin aikata magudi a zaben gwamnan jihar Osun da ke yankin kudu maso yammacin kasar.

'Yan adawar na zargin hukumar zaben ne saboda rashin fitar da sakamakon zaben da aka yi a ranar Alhamis don cike gibin da aka samu a makon jiya, da ya hana bayyana dan takaran da ya yi nasara.

'Yan takara 48 ne daga jam'iyyu dabam-dabam suka fafata a zaben, sai dai wadanda suka fi karfi su ne 'yan jam'iyyar APC mai mulkin kasar da kuma na babbar jam'iyyar adawa wato PDP.

Zaben na jihar Osun dai na zaman zakaran gwajin dafi ne ga manyan zabukan kasar da za a yi a watannin Fabrairu da kuma Maris na badi.