1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boye kudaden da aka sace a Najeriya a kasashen waje

Uwais Abubakar Idris MNA
October 5, 2021

Pandora Papers ta ambato wasu ‘yan siyasa su 10 a cikin jerin mutanen da suka kwashe kudadde tare da boye su a kasashen waje wanda wani binciken da ‘yan jaridu suka gudanar a kasashe 91 na duniya.

https://p.dw.com/p/41ImP
Pandora Papers | Symbolbild
Hoto: Zeljko Lukunic/PIXSELL/picture alliance

A tsanake ne dai fiye da 'yan jaridu 600 suka gudanar da wannan binciken da ake wa lakabi da Pandora Papers, suka bankado yadda 'yan siyasa da shugabanni suka boye makudan kudaden da suka kwasa daga kasashensu a asirce. Bincike ya ambato mutane 10 'yan Najeriya da suka hada da tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi wanda tuni ya musanta zargin bisa cewa shi bai aikata wani laifi ba. Akwai sauran 'yan Najeriya da suka hada da tsofaffin gwamnoni da ma wadanda ke kan mulki, da 'yan majalisar dattawa da 'yan kasuwa har da shugabannin addini da suka ki cewa uffan a kan zargin. Barister Buhari Yusuf ya bayyana abin da wannan ke nunawa.

"Wadannan taardu sun fito da abubuwa da dama da suka tayar da hankalin duniya gaba daya. Ambato wasu 'yan Najeriya a jerin masu sace kudin kasa su boye a kasashen waje na zama manuniya ga gwamnatin kasar ta bijiro da sabbin dokokin yaki da cin hanci da rashawa hade da hukunta duk wanda aka kama da wannan laifi."

Wasu 'yan Najeriya na a jerin masu sace kudin kasa su boye a kasashen ketare
Wasu 'yan Najeriya na a jerin masu sace kudin kasa su boye a kasashen ketareHoto: Zeljko Lukunic/PIXSELL/picture alliance

Bankado aikata cin hanci da sace kudin kasa a daidai lokacin da ake cara na yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya da ma kasashen duniya, na aika muhimmin sako a kan yadda kamfanoni na kasashen waje ke taimakawa wajen adana kudade na haramun a yanayi na an bar jaki ana dukan taiki. Comrade Isa Tijjani mai shairhi kan al'amurran yau da kullum na mai bayyana cewa "akwai matukar bukatar karfafa aikin hukumomin yaki da cin hanci don fallasa wannan badakala."

A bin jira a gani shi ne matakin da gwamnatin Najeriya za ta dauka sanin cewa a baya irin wannan bincike na Panama da ya bankado 'yan Najeriya babu wani mataki da aka dauka a kansu, to sai dai kifi na ganinka mai jar koma.