1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP: Atiku ya zabi Okowa a matsayin mataimaki

June 16, 2022

Dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya tsayar da gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mutumin da zai taimaka masa a zaben da ke tafe na 2023.

https://p.dw.com/p/4CpJL
Nigeria PDP Vizepräsident Kandidat Iyorchia Ayu
Hoto: PDP/Facebook

Dan shekaru 61 kuma gwamnan jihar Delta da ke yankin Niger Delta, Ifenyi Authur Okowa  ne dai Atikun ya amince domin taimaka masa a zaben na badi da ke zaman mai tasiri ga makomar yan lemar.

Okowan dai ya doke abokan karawarsa guda biyu Nyesom Wike da ke zaman gwamnan Rivers da Emmanuel Udom takwaransa na Akwa Abom wajen samun nasarar da jam'iyyar PDP ke fatan na iya kaita ga samun amincewa ta daukacin sassan tarrayar Najeriyar a fadar Sanata Bello Hayatu Gwarzo da ke zaman mataimakin shugaban jam'iyyar reshen arewa maso yamma da kuma yayi bayanin hanyoyin kai ga bullar ta Okowa.

To sai dai kuma ko wane tasiri zaben na Okowa ke iya yi ga kokarin 'yan lemar na kwace mulki, bulla ta Okowan na iya kaiwa ga yamutsar hazo cikin jam'iyyar da tun da farkon fari wasu a cikin 'ya'yanta suka rika ambaton gwamna Wiken bisa mukamin da ke zaman na biyu.

An dai kai ga ayyana bullar ta Okowa dai ba tare da halartar jiga jigan 'ya'yan jam'iyyar da suka hada da shi kansa sakatarenta na kasa da jami'in kudinta da ma wasu jami'an zartarwa na da dama da ke goyon baya ga Wiken.

Senata Umar tsauri dai na zaman tsohon sakataren jam'iyyar na kasa da kuma yace bullar Okowwan ba ta da tasirin hargitsa lamura a tsakanin yan lema na kasar.