1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Jam'iyyar PDP ta kwace mulki a zaben Osun

Abdoulaye Mamane Amadou
July 17, 2022

Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar da kuri'u mafi rinjaye a gaban abokiyar hamayyarta jam'iyyar APC mai mulkin jihar.

https://p.dw.com/p/4EFNu
Nigeria Benin City | Edo State Wahlen | Godwin Obaseki gewinnt
Hoto: Olukayode Jaiyeola/picture-alliance/dpa

Rahotanni daga jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya na cewar dan takarar jam'iyyar PDP mai adawa Adeleke Ademola ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a wannan Asabar.

Hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC ta ce Adeleke Ademola ya lashe kananan hukumomi 17 a yayin da babban abokin karawarsa na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya gwamna Adegboyega Oyetola ya samu nasa a kananan hukumomi 13.

Hukumar EFCC ta chafke wasu mutane uku da ta zarga da sayen kuri'ar masun zabe a na tsaka da zabe.

Zaben na gwamnan jihar na a matsayin zakara gwajin dafi a gabanin babban zaben Najeriya da ke tafe nan da wasu watanni bakwai masu zuwa.